Tuesday, November 14, 2023

BAYANI AKAN SANA'AR SAYAR DA DATA


 

DAN ALLAH KA KARANTA A NATSE


Kamar yadda nayi alkawarin koyawa muku yadda za ku fara kasuwancin data to insha Allah wannan shine darasin.


Domin gajarce wannan rubutun zan takaita bayani akan mafi muhimmancin abubuwanda ya kamata ku sani game da sana'ar data.


1-Zabar Amintattun shafukan VTU

2-Zabar masu Araha.

3-Monify.

Akwai shafukan VTU bila adadin a sahar nan kuma abune mai wuya tantance wannene ba na yaudara ba.


1=SIFFOFIN SHAFUKAN VTU MASU AMINCI

1-Ya kasance customer care na su 24/7 ne

2-Ya kasance suna da positive reviews daga custominsu

3-Ya kasance customer care din su suna responding da sauri.


2=ZABAR MASU ARAHA:- Sau tari shafukan VTU masu arahar wuce qima na scammers ne, misali; zaga wasu suna tallata farashin data da a hankalce ba zai yiwu ba; kamar ace MTN 1GB  SME 140 ko 150, ko ka ji sun ce NO DEPOSIT FEE wanda kaima ka san ko farashin company yafi hakan.

 

Daga cikin masu arha akwai masu siyarwa akan N207 har zuwa 220 to a wannan fashin ma saye da siyar ke iya cin riba.


3=MONIFY:- Monify wani tsarin hada-hadar kudi ne na yanar gizo da yake bawa masu saye da sayarwa ONLINE damar karba ko tura kudi a yanar gizo. A wannan tsarin duk VTU page mai iganci yakan yi amfani da shi domin bawa custominsu damar zuba kudade a wallet dinsu ta hanyar DEDICATED BANK ACCOUNT wanda da zarar ka tura kudi kai tsaye sai a wallet dinka.

Kuma ya kasance suna da channel sama da daya kamar MONIEPOINT, WEMA BANK da STERLING BANK.


VTU WEBSITES DA NAYI AIKI DASU KUMA NA TABBATAR DA INGANCINSU.

1=DATA STATION:- Su na da sauki da rahusa kuma Hausawa ne in ba iya magana da turanci zaka iya yi musu magana ko korafi da Hausa. Farashin 1GB N215 ne.

Danna nan domin yin rajista da su.


2=DATA PLUS:- Su ma dai suna da sauki kuma su ma Hausawa ne, farashin 1GB N211 ne.


Danna nan domin rajista da su.


3=RIMI DATA HUBS:- Kusan ma da su na fara aiki sai dai farashin ya fi na saman su nasu N215 ne amma na kwan 2 ban ziyarci shafin ba ta yiwu yanzun sun rage dan sau tari su kan rage farashi. Kuma su ma Hausawa ne.

Danna nan domin yin rajista dasu.


Akula:- Kamar yadda mu ka sani ba wata sana'a a duniya da bata da risks, sai dai risk din sana'ar data mai sauki ne kuma usually yakan afku daga mai sana'ar, Misali; mistake na number wajen turawa wani data ko wani ya kiraka bayan ganin tallar ka online yace ka tura masa daga baya ya tura ma kudi to in ka amince da shi kuma ya cuceka to ka ga zamu iya cewa daga gareka ne, duk da ita qaddara takan riga fata ne.

Allah ya tsare Ameen!


Idan da abinda baku gane ba kuna iya barin tamayoyinku a comment box. Mun gode.


Saturday, November 4, 2023

YADDA ZA KA MAGANCE MATSALAR MEMORY

 

Kamar yadda yake sanannen abuu ga kowannen mu cewa sau tari mu kan ajiye fayiloli (files) masu muhimmanci a gun mu, wanda sau da yawa da zaran mun rasa su kuma shikenan ba lallai ba ne mu sake samun su ba har abada.

Kamar yadda kowa ya sani cewa yanzun duniya tana ta samun cigaba ne ta fannin technology Wato (Kimiyya), hakan ne sa yanzu duk mai amfani da na'ura mai kwakwalwa (computer) ko wayar hannu (handset/smartphone) yana da damar ajiye kayakinsa a saman yanar gizo (internet), ta yadda da zaran Memorinka/wayarka ta/ya bata ko ya lalace zaka iya dawo da kayakin a duk lokacin da ka so. Saboda haka yanzu zan kawo platforms guda uku wadanda suka fi shahara kuma suka fi tsaro.

Gasu kamar haka:
1-Google Drive
2-Media Fire
3-BOx

1-GOOGLE DRIVE:- Shi google drive kamfanin google ne suka samar da shi kuma suke bawa duk me amfani da google account kyautar 15GB storage wato kusan kimani mega dubu goma sha biyar domin ajiye kayakinsu. Sai dai kuma idan wannnan filin bai isheka ba zaka iya sayen na kudi wato (premium).

Sai dai kuma idan wannnan filin bai isheka ba zaka iya sayen na kudi wato (premium).Sai dai kuma inda matsalarsu take shine idan ka dauki kimanin wata 6 bakayi amfanin da google account dinka ba to zasu dakatar da kai, kuma shikenan kayi asarar kayakinka.

Haka zalika kuma masu amfani da Vivo da kuma wasu nau'ikan Camons suna shan wahala domin wasunsu basa supporting din Google apps kuma basa bude Google servers.

Danna nan domin yin rajista

2-MEDIA FIRE:- Media fire shima wani nau'in cloud storage ne wanda yake bawa wadanda sukayi rajista da shi kyautar 10GB na storage wato mega dubu goma kenan.

Wannan platform kusan shine mafi sauqin sha'ani da baida wasu matsaloli masu yawa, kuma kusan kowane nau'in waya yana bude shi harma da wasu daga cikin keypads.Shima dai kamar Google drive zaka iya upgrading na space dinka, ma'ana zaka iya sayan na kudi ka qara da na kyauta idan bai ishe ka ba, haka kuma suna da REFERAL program wanda idan ka gayyato musu mutum 1 yayi rajista ta qarqashinka zasu baka 1GB wato mega dubu kenan.

Sannan shi zaka iya accessing na files dinka matuqar ba ka manta email address da password dinka ba ko da kuwa anyi banning email address dinka.Sai dai su kuma matsalarsu ba zaka yi batch download ba idan ba kayi upgrading zuwa pro ba.

Danna nan domin yin rajista

3- Box:-shima nau'in cloud storage ne, kuma daya daga cikin shahararru, shima idan kayi rajista zasu baka 10GB, kamar dai Media Fire, kuma shima zaka iya upgrading din shi zuwa pro, ma'ana zaka iya sayen wani space bayan na kyauta, sai dai su ma basu da referal program.Haka zalika suma suna da features din da dole sai inkana a pro membeship zaka iya samun wadannan features din, kamar su batch download, Url upload da dai sauran su.

Danna nan domin yin rajista

Insha Allahu zan kawo muku bayani akan Telegram, 4Shared, Ice drive, Yandex drive, One drive, Amazon drive, Mega, Degoo da Tera Box. Amma kafin nan in kun ji dadin wannan post din to kuyi mana like, comments da share domin qarfafa mana.

Mun gode.

Friday, November 3, 2023

YADDA ZA KA TURA SAƘO DA ƁOYAYYAR LAMBA

 


Kamar yadda muka sani har zuwa yau ba kamfanin sadarwan da ke bada damar tura saƙo da ɓoyayyar lamba, saboda haka ne yau na zo muku da wata hanya wacce za ba ku damar tura saƙonni da duk irin sunan da kuke so. Misali: HELLO, WELCOME, ko sunan ka suwancin ku ko ƙungiyar ku.

Wannan shi ake kira da BULK SMS , da wannan tsarin kamfanoni ke isarwa  kostomomin su saƙuna, kuma wani abun burgewa shi ne kana iya turawa sama da mutum 100 saƙo kala daya a lokaci guda, amma za a caje ka kuɗin kowane saƙon mutum ɗaya , Misali in za ja ₦4 a saƙo 1 to duk mutum 1 zai zama ₦4 kenan ka ga in ka turawa mutum 10 zai zama 4*10=40.

Akwai websites guda biyu da na aminta da su kuma akansu zamu yi magana duk da cewa suna da yawa sosai.

1- 80KOBOSMS :- Idan kayi registration da su kuma kayi funding kuɗi a wallet din ka to nan take zaka fara tura saƙo da duk kalar sunan da kake so ya bayyana ga wanda ka turawa saƙon. Danna nan domin yin rajista.

2- BULK SMS NIGERIA:- Su kamar wancan ne abin da kawai za ka yi shi ne ka yi rajista da su sannan kayi funding wallet na ka sai ka cigaba da tura saƙonni da duk kalar sunan da kake bukata.

Danna nan domin yin rajista.

80KOBOSMS YAFI SAUKIN FARASHI.

Like👍              Comment  💬        Share

Friday, June 2, 2023

YADDA ZA KA HANA KOWA YA KIRA KA SAI WANDA KA SO (CALL CONTROL)

A yau mun kawo muku video 📸 yadda zaku saita kiran wayar ku da yadda ba wanda zai kira ka sai wanda ka ke son ya kira ka, wato (Call control)


Za iya kallon video a nan ko ku je You tube Channel ɗinmu mai suna KIMIYYAH DA FASAHA TV


Thursday, March 2, 2023

YADDA ZA KA BUDE GMAIL ACCOUNT

 

GOGGLE MAIL ko GMAIL a takaice ya kasance shine kan gaba a dukkan Email providers, kuma shine e-mail provider daya tal da yake bawa masu amfani da shi filin ajiyar files ɗin su har kimanin 15 GIGA BYTES wato mega dubu goma sha biyar kenan.

Kuma ya kasance shine mafi tsaro kuma mafi saurin isar da  sakon a internet cikin sauki nan take, in kana da Google account zaka iya ajiye photo, videos, contacts, documents, credentials da duk wani abu da yake da muhimmanci a gare ka. Bugu da kari zai iya nuna maka duk inda wayar ka take koda ta bata matukar wannan email ya na kanta.

Yanzu sai mu je kai tsaye don sanin yadda ake bude Google account.

Da farko dai zaka shiga cikin browser  naka sai ka rubuta google.com amma ina baka shawarar yin amfani da CHROME.

Sai ka danna Go ko ➡ daga nan zai kai ka wannan shafin ⬇


Sai ka danna Sign In daga na zai kai ka wannan shafin ⬇

Sai ka sannan create account sai ka danna Next daga nan zai nuno ma wannan ⬇


Sai ka zabi "for my personal use" sai ka danna Next zai kai ka shafi na gaba ⬇


Sai ka cike wadannan guraren da aka sanya wa jar alama alama sai ka danna Next



Sai ka saka lambar wayar ka sannan ka  danna Next zai wuce shafi na gaba ⬇


Sai ka danna I agree shikenan Ka kammala hada GMAIL ACCOUNT ɗin ka.

Kuna Ku na iya ajiye mana tambayoyin ku a a cikin comments.

Like👍               Share💓               Comment 💬   

Wednesday, February 22, 2023

HOW TO GET 1GB OF FREE DATA FOR ALL NETWORK


As we always surf the internet and some of us are always busy searching for articles on how to get free data and finally end up wasting our data bundle without having one.

Calm down! We come up with the best system for you to get free Data worth 1GB within every 48 hours (2 days). It's as simple as taking coffee. In this system, there're two steps and you can choose any one that suits you. Below are the steps ⬇

STEP 1

 Click the link HERE to register with PALMPAY and make sure you authenticate your account by binding your account number or NIN number to it so that they will verify your account within 24-48 hours.

 After registration send your number and the name you registered with it to this number on WhatsApp +234 813 071 4054 to receive your 1GB.

STEP 2

 By inviting your friends to buy our DATA or CONVERTING THEIR AIRTIME TO CASH.

Invite 5 of your friends to buy our DATA, the invitation should be this way.

 Ask your friends to chat with this  +234 813 071 4054 WhatsApp number if they need to buy Data or Convert their airtime to cash.

Then send the names of the people you invited to the above number.

Like👍                 Share💓               Comment💬

Friday, February 17, 2023

SHARPENCY DATA AND AIRTIME SERVICES


Muna sayar da DATA da AIRTIME akan farashi mai sauqi, kuma tsawon lokacin ta kwana 30 ne.

Kuma muna converting na MTN AIRTIME zuwa CASH mu tura ma zuwa bankin ka, kai tsaye kuma akan farashi mai sauqi.

Ga waɗanda suke buqata sai su tura kuɗin ga wannan asusun, sai su yi mun magana ta inbox.

Account Name: Abdullahi Bulbuli Umar
Account Number: 8064503400
Bank Name: Palmpay

MTN
500MB N200
1GB N300
2GB N600
3GB N800
5GB N1200
10GB N2400

AIRTEL
500MB N200
1GB N300
2GB N600
5GB N1200
10GB N2300

9MOBILE
1.1GB N550
2GB N950
3GB N1300
4GB N1500

GLO
1.5GB N650
2.9GB N1100

BAYANI AKAN SANA'AR SAYAR DA DATA

  DAN ALLAH KA KARANTA A NATSE Kamar yadda nayi alkawarin koyawa muku yadda za ku fara kasuwancin data to insha Allah wannan shine darasin. ...