Saturday, November 4, 2023

YADDA ZA KA MAGANCE MATSALAR MEMORY

 

Kamar yadda yake sanannen abuu ga kowannen mu cewa sau tari mu kan ajiye fayiloli (files) masu muhimmanci a gun mu, wanda sau da yawa da zaran mun rasa su kuma shikenan ba lallai ba ne mu sake samun su ba har abada.

Kamar yadda kowa ya sani cewa yanzun duniya tana ta samun cigaba ne ta fannin technology Wato (Kimiyya), hakan ne sa yanzu duk mai amfani da na'ura mai kwakwalwa (computer) ko wayar hannu (handset/smartphone) yana da damar ajiye kayakinsa a saman yanar gizo (internet), ta yadda da zaran Memorinka/wayarka ta/ya bata ko ya lalace zaka iya dawo da kayakin a duk lokacin da ka so. Saboda haka yanzu zan kawo platforms guda uku wadanda suka fi shahara kuma suka fi tsaro.

Gasu kamar haka:
1-Google Drive
2-Media Fire
3-BOx

1-GOOGLE DRIVE:- Shi google drive kamfanin google ne suka samar da shi kuma suke bawa duk me amfani da google account kyautar 15GB storage wato kusan kimani mega dubu goma sha biyar domin ajiye kayakinsu. Sai dai kuma idan wannnan filin bai isheka ba zaka iya sayen na kudi wato (premium).

Sai dai kuma idan wannnan filin bai isheka ba zaka iya sayen na kudi wato (premium).Sai dai kuma inda matsalarsu take shine idan ka dauki kimanin wata 6 bakayi amfanin da google account dinka ba to zasu dakatar da kai, kuma shikenan kayi asarar kayakinka.

Haka zalika kuma masu amfani da Vivo da kuma wasu nau'ikan Camons suna shan wahala domin wasunsu basa supporting din Google apps kuma basa bude Google servers.

Danna nan domin yin rajista

2-MEDIA FIRE:- Media fire shima wani nau'in cloud storage ne wanda yake bawa wadanda sukayi rajista da shi kyautar 10GB na storage wato mega dubu goma kenan.

Wannan platform kusan shine mafi sauqin sha'ani da baida wasu matsaloli masu yawa, kuma kusan kowane nau'in waya yana bude shi harma da wasu daga cikin keypads.Shima dai kamar Google drive zaka iya upgrading na space dinka, ma'ana zaka iya sayan na kudi ka qara da na kyauta idan bai ishe ka ba, haka kuma suna da REFERAL program wanda idan ka gayyato musu mutum 1 yayi rajista ta qarqashinka zasu baka 1GB wato mega dubu kenan.

Sannan shi zaka iya accessing na files dinka matuqar ba ka manta email address da password dinka ba ko da kuwa anyi banning email address dinka.Sai dai su kuma matsalarsu ba zaka yi batch download ba idan ba kayi upgrading zuwa pro ba.

Danna nan domin yin rajista

3- Box:-shima nau'in cloud storage ne, kuma daya daga cikin shahararru, shima idan kayi rajista zasu baka 10GB, kamar dai Media Fire, kuma shima zaka iya upgrading din shi zuwa pro, ma'ana zaka iya sayen wani space bayan na kyauta, sai dai su ma basu da referal program.Haka zalika suma suna da features din da dole sai inkana a pro membeship zaka iya samun wadannan features din, kamar su batch download, Url upload da dai sauran su.

Danna nan domin yin rajista

Insha Allahu zan kawo muku bayani akan Telegram, 4Shared, Ice drive, Yandex drive, One drive, Amazon drive, Mega, Degoo da Tera Box. Amma kafin nan in kun ji dadin wannan post din to kuyi mana like, comments da share domin qarfafa mana.

Mun gode.

No comments:

Post a Comment

BAYANI AKAN SANA'AR SAYAR DA DATA

  DAN ALLAH KA KARANTA A NATSE Kamar yadda nayi alkawarin koyawa muku yadda za ku fara kasuwancin data to insha Allah wannan shine darasin. ...