DAN ALLAH KA KARANTA A NATSE
Kamar yadda nayi alkawarin koyawa muku yadda za ku fara kasuwancin data to insha Allah wannan shine darasin.
Domin gajarce wannan rubutun zan takaita bayani akan mafi muhimmancin abubuwanda ya kamata ku sani game da sana'ar data.
1-Zabar Amintattun shafukan VTU
2-Zabar masu Araha.
3-Monify.
Akwai shafukan VTU bila adadin a sahar nan kuma abune mai wuya tantance wannene ba na yaudara ba.
1=SIFFOFIN SHAFUKAN VTU MASU AMINCI
1-Ya kasance customer care na su 24/7 ne
2-Ya kasance suna da positive reviews daga custominsu
3-Ya kasance customer care din su suna responding da sauri.
2=ZABAR MASU ARAHA:- Sau tari shafukan VTU masu arahar wuce qima na scammers ne, misali; zaga wasu suna tallata farashin data da a hankalce ba zai yiwu ba; kamar ace MTN 1GB SME 140 ko 150, ko ka ji sun ce NO DEPOSIT FEE wanda kaima ka san ko farashin company yafi hakan.
Daga cikin masu arha akwai masu siyarwa akan N207 har zuwa 220 to a wannan fashin ma saye da siyar ke iya cin riba.
3=MONIFY:- Monify wani tsarin hada-hadar kudi ne na yanar gizo da yake bawa masu saye da sayarwa ONLINE damar karba ko tura kudi a yanar gizo. A wannan tsarin duk VTU page mai iganci yakan yi amfani da shi domin bawa custominsu damar zuba kudade a wallet dinsu ta hanyar DEDICATED BANK ACCOUNT wanda da zarar ka tura kudi kai tsaye sai a wallet dinka.
Kuma ya kasance suna da channel sama da daya kamar MONIEPOINT, WEMA BANK da STERLING BANK.
VTU WEBSITES DA NAYI AIKI DASU KUMA NA TABBATAR DA INGANCINSU.
1=DATA STATION:- Su na da sauki da rahusa kuma Hausawa ne in ba iya magana da turanci zaka iya yi musu magana ko korafi da Hausa. Farashin 1GB N215 ne.
Danna nan domin yin rajista da su.
2=DATA PLUS:- Su ma dai suna da sauki kuma su ma Hausawa ne, farashin 1GB N211 ne.
Danna nan domin rajista da su.
3=RIMI DATA HUBS:- Kusan ma da su na fara aiki sai dai farashin ya fi na saman su nasu N215 ne amma na kwan 2 ban ziyarci shafin ba ta yiwu yanzun sun rage dan sau tari su kan rage farashi. Kuma su ma Hausawa ne.
Danna nan domin yin rajista dasu.
Akula:- Kamar yadda mu ka sani ba wata sana'a a duniya da bata da risks, sai dai risk din sana'ar data mai sauki ne kuma usually yakan afku daga mai sana'ar, Misali; mistake na number wajen turawa wani data ko wani ya kiraka bayan ganin tallar ka online yace ka tura masa daga baya ya tura ma kudi to in ka amince da shi kuma ya cuceka to ka ga zamu iya cewa daga gareka ne, duk da ita qaddara takan riga fata ne.
Allah ya tsare Ameen!
Idan da abinda baku gane ba kuna iya barin tamayoyinku a comment box. Mun gode.

No comments:
Post a Comment